Wednesday, 14 September 2016

Ku manta da raba kasa  -Sakon Buhari zuwa ga yan kudancin Najeriya

Shugaban ya yi wannan kiran ne yayinda masu bautawa kasa da suke aiki a karamar hukumarsa ta Daura wajen su dari suka kai masa gaisuwa gidansa. Shugaba Buhari ya sake jaddada anniyarsa na tabbatar da hadin kan kasar da cigabanta.

Daga bisani sai shugaban ya koma kan ‘yan Niger Delta din cewa su fada wa ‘yanuwansu da suke neman kafa kasar Biafra su manta da ita, wato abu ne da ba zai sabu ba, wai bindiga a ruwa.

Yace a matsayinsa na tsohon janar ya taka daga Degema, wani gari dake kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru. Haka kuma yayi watanni talatin yana yakin Najeriya da Biafra, yakin da ya lakume mutane kimanin miliyan biyu.

Yace shugabanninsu sun turasu su yaki Biafra ba wai domin kudi ba ko man fetur amma sabili da Najeriya.

Saboda haka idan wasu shugabannin kasar sun gaza ba ‘yan Najeriya suka gaza ba, inji Buhari.

Yace ku fadawa ‘yanuwanku dole mu cigaba da tafiya tare mu gina kasarmu. Tana da girma kuma albarkatunta sun ishemu duka, inji shugaba Buhari.

Da yayi magana a madadin ‘yan bautawa kasar jami’insu dake Daura Mr. Egbewumi Adebolu ya godewa shugaban da yadda ya karramasu da karbarsu. Yace yawancin masu bauta wa kasar sun yadda da shirin shugaban na rage rashin aikin yi.

Mr. Adebolu ya kara godewa shugaban da kyautar shanu da buhunhunan shinkafa da kudi da ya basu domin su ji dadin bikin salla.

The post Ku manta da raba kasa  -Sakon Buhari zuwa ga yan kudancin Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cYlidl
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...