Wani mutun a fusace ya sanya matarsa a kasuwar nan ta ebay a shafin yanar gizo saboda acewar sa bata kula da shi.
Shi dai mutumin mai sune Simon O’Kane wanda kuma dan garin Wakefield ne ya sanya matar tasa a shafin yanar gizon na ebay.
Mutumin ya shaida wa duniya cewar matar tasa mai suna Leandra bata kula da hakkokin sa yanda ya kamata a matsayin mijin ta.
A shafin na siyarwar, mijin mai shekaru 33 a duniya ya sa ma matar farashi amma daga baya sai yayi ta kara farashin inda yanzu haka matar ta kai kimanin £65,880 watau N32,940,000 a cikin kwanaki 2 kacal.
Simon yace wanda wata rana bayan na dawo daga aiki a gajiye kuma ba da wata isassar lafiya ba amma matar tawa mai shekaru 27 yanzu sai tayi burus dani.
Ita kuma watar tace: “Gaskiya banji dadin abun da yayi mun ba don ko yanzu haka duk inda na je dariya akeyi mun ana aibata ni.”
no
Shin mai karatu wannan hauka ne ko wayewa?
The post Miji ya sa matar sa a kasuwa saboda bata kula da shi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cYkN3j
via IFTTT
No comments:
Post a Comment