Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa har yanzu bai ga wani mataki na zahiri da gwamnati ta dauka na farfado da tattalin arzikin Nijeriya wanda a halin yanzu ya karye.
Saraki ya kuma tabbatar da cewa majalisar za ta gayyato masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki na gwamnatin Buhari don su yi wa majalisa cikakken bayani game da matakan da suke dauka na farfado da tattalin arzikin Nijeriya inda ya nuna cewa za su ba Buhari shawarwari kan yin waje rod da duk wani Minista da gaza kan aikinsa.
Ya kara da cewa tun da ya shiga siyasa a shekarar 1999 bai taba ganin irin wannan yanayin kunci da al’ummar Nijeriya ke ciki ba.
The post Bukola Saraki ya soki tsarin tattalin arzikin Shugaba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cYkwx3
via IFTTT
No comments:
Post a Comment