Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya roki yan Najeriya dasu cigaba da hakuri da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarin da yake yin a fitar da kasar nan daga kangin karyewar tattalin arziki.
Gwamnan ya amsa cewa lallai tattalin arzikin kasa a lalace yake, inda ya kara da bayyana tabbacin shugaba Buhari nada dukkan shika shikan da ake bukata daga shugaba musamman wajen fitar da kasar daga matsalar tattalain arziki data fada.
Gwamna Bello ya kara da bukatar yan Najeriya kada su karaya da gwamnatin Buhari dasu cigaba da sa ran komai zai gyaru nan bada dadewa ba. Jaridar Vanguard ta ruwaito gwamnan na bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jihar Kogi bayan gudanar da Sallar Idi a babban masallacin Felele, inda Gwamna Bello ya kara da cewa gwamnatin jihar Kogi na aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya wajen ganin ta sama ma matasa aikin yi.
KU KARANTA:An jefi Gwamna Yahaya Bello
Rahoton ya ruwaito Bello yana cewa gwamnati zata tallafa ma sama da matasa da mata 100,000 ta hanyar fitar da wasu shirye shiryenta, yace “gwamnati tat a matasa ce, nan bada dadewa ba zamu fitar da wani tsarin daukan aiki don rage radadin zaman banza, tare da kare matasan mu daga shiga hannun yan siyasan Abuja daga amfani da su wajen tada hankulan al’umma. “muna iya kokarin mu wajen gayyatar masu zuba jari zuwa garin mu, amma fa idan babu zaman lafiya da hadin kai a tsakanin matasa, jihar ba zata ci gajiyar wannan dama ba”
Shi ko babban limamin Lokoja, Alhaji Abdullahi Baba a yayin da yake huduba yace ya zama wajibi ga duk musulmi ya kasance mai kyawawan halaye, wannan shi ne manufar Idi. Sa’annan ya bukaci musulmai da su so junansu tare da zama lafiya da juna.
Kazalika ministan tama da karafuna Kayode Fayemi da kaakakin majalisar wakilai Mudashiru Obasa suma sun bukaci yan Najeriya dasu zauna lafiya da juna, tare da nuna soyayya da tausayi ga juna.
The post Gwamna Bello ya roki yan Najeriya dasu mara ma Buhari baya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cnlmrt
via IFTTT
No comments:
Post a Comment