Friday 16 September 2016

Zargin almundahana: Shema ya mika kansa ga hukuma

– Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahin shehu Shema ya mika kansa ga hukuma

– Wannan na faruwa ne bayan kwana 2 da hukumar EFCC ta alanta neman shi ruwa a jallo

Hukumar EFCC tana neman tsohon gwamna ruwa a jallo

Hukumar EFCC tana neman tsohon gwamna ruwa a jallo

Tsohon gwamnan jihar Katsinan da hukumar hana Almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta alanta neman sa ruwa a jallo ya mika kansa ga hukuma.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa shema ya isa ofishin hukumar EFCC da ke Abuja da misalin karfe 9:30 na safiyar yau juma’a, 16 ga wata Satumba.

An alanta neman tsohon gwamnan ne a ranan laraba da laifin karkatar da kudin al’umma N18 billion zuwa asusun bankin sa.

Mai Magana da yawun shi Oluwabusola Olawale,yace Shema ya mika kansa ga hukuma saboda mutum ne wanda ke girmama doka kuma bashi da abin tsoro.

KU KARANTA: Jihohi 6 da basu girgiza da karayar tattalin arziki ba

Game da shi, Shema ya mika kansa zuwa ga hukumar hana rashawan duk da cewan basu masa adalci ba wajen kiransa. Har yanzu dai ba’a sani ba ko Shema ya je da lauyoyinsa ne ofishin .

Zaku tuna cewa hukumar EFCC ta ce tana neman Shema ruwa a jallo ne saboda ta dade tana mika masa goron gayyata akan tuhumece-tuhumcen da ake masa amma bai amsa ba.

A mayar da martanin kar ta kwana, Shema ya musanta zargin da ake masa kuma y ace shi ba gudu yayi ba. Ya sifanta sanarwan neman sa a jallo a matsayin shirme da wulakanci. Yace abin ya bashi kunya kuma bai ji dadi ba a ce ana neman sa ruwa a jallo.

The post Zargin almundahana: Shema ya mika kansa ga hukuma appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2ctRKDA
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...