Wednesday, 14 September 2016

Wani fasto ya mutu akan minbari

Wani fasto mai suna Caleb Sifuna, ya zube yayinda yake magana akan minbari.

Jaridar Tuko ta bada rahoton cewa Faston cocin Free Salvation Life Ministries da ke Kanduyi, Bungoma county ,ya fadi ne daga inda yake zaune gab da ya fara hudubarsa.

Lagos. Nigeria. September 2007 The faithful gather in their thousands for an overnight service at the Redeemed Church of Christ.

Yana shirin gabatar da waazi ne ga jama’arsa sa mutuwa ta zo masa. An kai shi asibiti da gaggawa domin ceto ransa amma ina, ya rigaya da mutuwa.

Yayinda ake tabbatar da mutuwarsa , Bishap Mr Nahashon Khaemba yace Mr Sifuna bai dade daga jinyan rashin lafiya ba kuma wannan shine huduban farko da zai bada bayan farfadonwan sa.

KU KARANTA:Ministan Abuja zai kori Almajirai da mabarata daga Abuja

 “Munyi rashin amini da kuma mai bauta. Babu wanda zamu tuhuma da mutuwarsa. Sai dai mu gode ma Allah saboda mun san yayi masa tanadi mai kyau. Cocin na juyayi amma mun san ubangihi yafi mu sani.

 “Tunda ya tashi daga rashin lafiya, bai yi kukan wani ciwo ba kuma babu alamun cewa bashi da lafiya. Naki mamakin mutuwan shi a yanzu.

The post Wani fasto ya mutu akan minbari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cnnbok
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...