Friday, 16 September 2016

Tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba ya taimaki dalibai 5000 a makaranta

-Tsohon dan wasan Chelsea ya taimaki dalibai 5000 na kasar Ivory cost                  

-Dan wasan ya Saya ma dalibai kayan makaranta

Tsohon dan wasan gaba na Ivory cost da Chelsea ya cigaba da ayyukan shi na alheri a matsayin dan kwallon da yafi kowa taimako.

Waccan shekarar, dan wasan ya taimakama daliban makarant 5000 da kayan karatu a kasar Ivory cost a sabon zangon karatu.

Didier Drogba donates school kits

Didier Drogba ya taimaki daliban makaranta.

Kayan da aka taimaki daliban marasa galihu da su, sun hada da littafan karatu, jaka, kayan rubutu, kayan yin lissafi, robar ruwa da abubuwan amfani a bayan daki.

Kungiyar taimako ta didier Drogba, wadda aka saka ma sunan sa kuma aka kafa shekara ta 2007, wadda kudurinta shine taimakon mutanen Ivory cost ta Fannin lafiya da Ilimi.

The post Tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba ya taimaki dalibai 5000 a makaranta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cPeYpv
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...