Shugaba Muhammadu Buhar ya isa birnin Abuja a yau din nan 14 ga watan Satumba daga garin sa na haihuwa Daura bayan shafe kwanakin hutun sallah a can.
Buhari ya samu rakiyar Gwamnan jihar ta Katsina dama sauran mukarraban gwamnatin a yau a filin sauka da tashin jiragen saman Katsina da misalin karfe 11na safe.
A can Abuja kuma ya samu tarbar ministan Abuja Muhammed Musa Bello da kuma Sifeto Ganar na yan sandan Najeriya Ibrahim Idris.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bi sahun miliyoyin Musulman duniya, inda ya halarci Sallar Idi, a mahaifarsa, dake Daura a jihar Katsina.
Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar da Magajin Daura, Alhaji Musa Umar na cikin wadanda suka gabatar da Sallah a
filin Idin na Daura.
The post Shugaba Buhari ya koma bakin aiki bayan hutun sallah appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cnlcQF
via IFTTT
No comments:
Post a Comment