Friday, 16 September 2016

Rikicin jam’iyar APC ya kazanta a jahar Delta

– Rikicin dake faruwa a jam’iyar APC a jahar Delta ya girmama                                

– Dattawan jam’iyar sun cire zababbin shugabanni masu ci                                       –

– An nada komitin rikon kwarya.

Lamarin rikicin jam’iyar APC shiyar jahar Delta ya girmama, wanda zaman lafiya a yanzu haka ya zama barazana a jam’iyar.

A rohoton da muka samu a breaking time ya bayyana mana cewa rikicin da Ke faruwa na jam’iyar APC a jahar Delta ya zama abun damuwa wanda ya janyo har dattijai da jiga-jigan jam’iyar suka cire zababbin shugabanni kungiyar masu ci.

apc changes

Jiga-jigan jam’iyar sun cire zababbun shugabanni ranar alhamis 15 ga watan Satumba, suka kuma nada komitin rikon kwarya da kula dan harkokin jam’iyar. Kamar yadda dattijan jam’iyyar suka nuna, komitin ze kula da haekokin jam’iyar har sai lokacin da dattijan jam’iyar na kasa suka canza sababbin zababbun shugabanni.

Sakamakon da taron da akayi a gidan shugaban dattawan jam’iyar APC na jahar, Sanata Francis Spanner Okpozo a Ozoro, karamar hukumar isoko ta arewa, dattijan da jiga-jigan sun yanke shawarar nada kwamitin rikon kwarya a karshen tarurrukan da suka fara tun watan yunin shekarar nan.

Sanata Okpozo ya Kira taro a watan yuni a gidansa inda aka yarda da nada komitin rikon kwarya, wanda zasu maye gurbin Jones Erue shugaba mai ci bayan kuri’ar da dattijan suka jefa ta rashin amincewa da shugabancin sa.

Yayin da ake rantsar da komitin, Okzopo yace dattijai da jiga-jigan jam’iyar suka yanke hukuncin bayan babbar kotun Asaba ta tuge su da shugabancin jam’iyar watan nin da suka gabata, inda yace ba zamu nade hannu mu zura ido mu cigaba da kallon haka ba.

The post Rikicin jam’iyar APC ya kazanta a jahar Delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cjEbJ4
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...