Friday, 16 September 2016

Mutane 5 yan gida daya sun rasu ranar tarewa a sabon gida

Al’ummar kauyen Isale-oyo na karamar hukumar Atiba dake jihar Oyo sun shiga halin firgici a ranar Laraba 14 ga watan satumba, lokacin da suka tsinci gawawwakin wasu yan gida daya da suka rasu gaba dayansu a wani hali daya dimauta su.

Tambarin yan sandan Najeriya

Mamatan sun hada da Miji da amaryarsa da yayansu biyu sai dan uwansu daya kawo musu ziyara. An samu gawawwakin nasu ne a sabon gidan da amaryar mutumin ta kammala ginawa a yan kwanakin nan.

Iyalan sun rasu ne a ranar da suka tare a gidan, ranar talata 14 ga watan satumba, inda suka shirya gudanar da walimar tarewa a ranar laraba. A lokacin da mijin ya umarci uwargidarsa data biyo su sabon gidan, sai ta ki. Iyalan mutumin sun gudanar da shagulgulan Sallah tare da yan’uwa da abokan arziki, daga nan ne mutumin ya gayyace su dasu dawo ranar laraba don halartar walimar tarewa sabon gidansu washegari.

KU KARANTA:Sherrif ya ki amincewa da fitar da Ize-Iyamu

Makwabta, yan’uwa da abokan arzikin mutumin sun isa gidan da safiyar ranar laraba don halartan walimar, amma sai suka tarar da gidan a kulle, bayan kwankwasa gidan da suka yi suka ji shiru ne, sai suka yanke shawarar  balla kofar gidan inda aka tarar da gawawwakinsu. Wani makwabcinsu daya nemi a boye sunan sa ya kwatanta lamarin tamkar wani shirin fim. “abin tausayi ne

Makwabta sun ce a ranar talata an hangi mamacin yana ta wasa da yayan makwabtan shi, kuma ya gaisa da iyayensu duk a cikin murnan shagalin Sallah. Sai dai DPO na yankin, Atiba Sadiq Maye ya tabbatar da faruwar lamarin, sa’nnan ya kara da cewa mamatan sun rasu ne daga hayakin janareto da suka shaka yayin da suke barci. An garzaya da gawawwakinsu zuwa dakin ajiye gawa na asibitin jihar Oyo.

The post Mutane 5 yan gida daya sun rasu ranar tarewa a sabon gida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cubnR5
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...