Friday 16 September 2016

Kotu tayi watsi da karan da ke kalubalantan nada Hameed Ali

Wata babban kotun tarayya da ke zaune a jihar legas tayi watsi da karan da ke kalubalantan nadin Kanal Hameed Ali a matsayin kamtrolan hukumar Kastam da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.

kotu

Kotu

Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa game da Jastis Saleh Hassan, wanda shine Alkali mai shari’a, kotun bata da karfin amsa irin wannan kara.

News Agency of Nigeria (NAN) ta bada rahoton cewa Wani mai himmar aiki, Ebun-Olu Adegboruwa, ya shigar da karan gaban Jastis Saleh Hassan a watan nuwamban 2015.

KU KARANTA: Rikicin jam’iyar APC ya kazanta a jahar Delta

Mr. Adegboruwa wanda ya nemi kotu da ta warware nadin hammed Ali , ya nemi fassaran cewa shin shugaban kasa na da karfin nada duk wanda yaso a matsayin komtrola janar ba tare da bin dokar Section 3 of the Official Gazette ba.

Kanal Hameed Ali ya mallaki digri da mastas a ilimin barandanci kuma ya taba gwamnan jihar Kaduna daga 1996-1998 karkashin gwamnatin sojan Janar Sani Abacha.

The post Kotu tayi watsi da karan da ke kalubalantan nada Hameed Ali appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cQTpHN
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...