Friday, 16 September 2016

Kamfanin Arik ya kori dan kasa ya dauki bature

Wani ma’aikacin jirgin sama ya zargi kamfani jiragen sama na Arik Air da wariyar launin fata, a inda ya kori wani matukin jirginsa, ya kuma dauko farar fara daga waje alhalin, ga kuma kin biyan albashi.

arik 2

Wani ma’aikacin kamfanin Arik mai zirga-zirgar jiragen sama mai zaman kansa a Najeria, ya rubuta wata budaddiyar takardar koke ga kungiyar kwadago ta kasa kan wariyar launin fata da nuna fifiko da kamfanin ya ke yi.

Mutumin wanda ya ki a bayyana sunansa, ya rubuta takardar koken ne ga kafar yada labarai ta Naij.com ya na mai cewa, Kamfanin jiragen sama na Arik Air a kwanan nan ya kori wani matukin jirgin sama na kamfanin saboda ya nemi a biya shi albashinsa na watanni uku da ya ke bi.

Amma a maimakon kamfani ya biya shi, sai ya kore shi daga aikin dungurun-gum, ya kuma maye gurbinsa da wani farar fata, budaddiyar takardar koken ta kuma ce, saboda yawan take hakkin ma’aikata, kamfanin ba ya kaunar a kafa kungiyar kwadago.

KU KARANTA KUMA:

Marubucin takardar ya ci gaba da bayanin cewa, ‘yan bangaren gyaran jirgi a kamfanin sun taba yunkurin kafa kungiyar kwadago saboda kin biyan bashin albashin da ya ke yi , amma kamfanin na Arik ya sallamesu.

Mai tarkardar koken ya kuma kara da cewa, duk da cewa kamfanin na daya daga cikin kamfanonin jirage da ke  jigilar fasinjoji da yawa a ciki da kuma wajen kasar nan, amma ba ya biyan albashin ma’aikatansa na Najeriya a kan kari.

Duk da cewa kin biyan albashin na yi musu ciwo, a cewar takardar, amma daukar farar fata daga waje a gurbin ‘yan kasa ya fi musu ciwo, don haka mai takardar ya ke rokon hukumomi da kuma kungiyar kwadago da su yi wani abu a kai.

 

 

The post Kamfanin Arik ya kori dan kasa ya dauki bature appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cjEfbU
via IFTTT

No comments:

Post a Comment

LinkWithin

Related Posts Plugin for WordPress, Blogger...