Tsohon shugaban Jonathan ya kai wa Babangida da kuma Abdussalam Abubakar ziyara a Minna a inda ya gana da kuma tattauna da kowannesu
Jonathan da Abdulsalami Abubakar a yayin ziyarar
A ranar Lahadi 13 ga watan Satumba ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai ziyarci tsaffin shugabannin kasar na soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Abdussalam Abubakar a inda ya yi wata ganawar sirri da kowannesu. Ga wasu abubuwa 4 da ake hasashen tsohon shugaban ya tattauna da takwarorin nasa a kai.
KU KARANTA KUMA: Laifukan Jonathan da Tampolo a yankin Niger Delta
1. Yaki da cin hanci da rashawa na Buhari: Wasu na rade-radin cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da yaki da cin hanci da rashawa na shugaba Buhari ba, da yadda kuma yadda zai shafi tsohon shugaba Jonathan musamma ta bangaren matarsa Patience.
2. Zaban jihar Edo: Dage zaben jihar Edo da makwanni 2 ya janyo ce-ce-ku-ce a inda gwamnatin PDP ta ke zargin Buhari da dagawa domin aikata makudi.
3. ‘Yan ta da kayar baya na Niger Delta: Babu mamaki ganawar da tsaffin shugabannin ta tabo batun yawaitar hare-haren tsagerun Niger Delta da zargin cewa da hannun Jonathan da kuma Jam’iyyarsa ta PDP duk da cewa ya musanta hakan.
4. Batun lafiyar Babangida: A ‘yan watanni da suka wuce ake ta rade-radin cewa ciwon tsohon shugaban kasa Babangida ya ta’azzara, ta yadda ba ya iya zuwa ko ina, hakan ta fito fili ne a lokacin da ya je walimar Mai shari’a Fati Abubakar a inda ya kasa tafiya sai da taimako.
The post Gananawar Jonathan da Babangida da Abdussalam appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2ceTL8R
via IFTTT
No comments:
Post a Comment