Wasu rahotanni daga Pakistan na cewa wani dan kunar bakin wake ya hallaka kimanin mutane 16 ya kuma jikkata wasu 35 a yayin Sallar Juma’a a arewa maso yammacin kasar.
Jami’an gwamnati a yankin da abin ya faru sun ce, harin kunar bakin waken ya faru ne a kauyen Butama a lardin Mohand da ke kan iyakar kasar da Afgahnistan, inda sojoji ke fada da mayakan kungiyar Taliban.
Rahotanni na cewa, wani babban jami’in gwamnati kuma shugaban kabilar yankin ya ce, “ana tsaka da Sallar Juma’a ne a masallacin kauyen a lokacin da dan kunar bakin waken ya ta da bam din da ke jikin sa, a inda ya hallaka kansa da kuma wasu mutane 16, ya kuma jikkata wasu 35”.
KU KARANTA KUMA: Alakar Fulani makiyaya da hare-hare a Enugu
Masu aikin ceto gami da ‘yan sanda sun garzaya wurin, yayin da ake ta kokarin kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin yankin da kuma asbitocin Bajaur, da Charsadda, da kuma Pehwar, domin karbar magani.
Babu dai wanda ya dauki alhakkin kai harin a nan take, sai dai ‘yan kungiyar Taliban ta kasar ta saba kai hare-hare a kan wuraren taron jama’a kamar Kotuna, da Makarantu, da kuma Masallatai a kasar, harin kuma ya zo a lokacin da Firayi ministan kasar Nawaz Shariff ya yi alkawarin kawo karshen ‘yan ta da kayar baya da kuma ‘yan ta’adda.
The post Dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 16 a Masallachi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cugH74
via IFTTT
No comments:
Post a Comment