Kimanin tsagerun Niger Delta hamsin ne da suka mallaki matatun mai ba bisa ka’ida ba jami’an tsaro na farin kaya na NSCDC suka damke a jihar Rivers.
Hukumar tsaron ta ce kimanin matatun mai goma sha biyar ne aka lalata a wurare daban daban a yakin Niger Delta.
Kwamadan hukumar tsaron Abdullahi Muhammad, a wata ganawarsa da manema labarai, a Abuja, ya ce wadanda ake zargin an damke su ne ranar laraba, da dare, a wani aiki na masamman da jami’an hukumar suka gudanar a jihar Rivers.
Ya kara da cewa ana tantance wadanda aka damken domin tabbatar da masu hannu a fashe fashe bututun mai a yankin na Niger Delta. Duk wanda aka samu da hannu in ji kwamandan za’a tuhumeshi da laifin yiwa kasa zagon kasa.
The post An bankado haramtattun matatun mai da dam a jihar Ribas (Kalli Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2d48134
via IFTTT
No comments:
Post a Comment